Dangantaka tsakanin Misra da Tanzaniyya
Alhamis, 10 Janairu, 2019
Dangantaka tsakanin Misra da Tanzaniyya

Takaitaccen Tarihi:

Dangantakar tsakanin kasar Misra da kasar Tanzaniyya ta fara tun shekara ta 1962, inda kyakkyawan dangantaka ta hada tsakanin shugabanni guda biyu; Jamal Abdul Nasir da Nyerere, wannan danagantaka mai karfi ita ce ta cigaba da kasancewa har zuwa wannan lokacin.

Dangantaka mai karfi ta hada tsakanin kasashen guda biyu, inda hakan ya haifar da samun taimakekeniya tsakaninsu a dukkan fannoni, kwamiti na musamman tsakanin kasar Misra da kasar Tanzaniyya suka yi tarayya a ciki, suna haduwa lokaci-lokaci; domin tattauna shawarwari akan cigaba da hanyoyin da za a habaka wannan dangantakar ta fannin kasuwanci da tattalain arziki da al’adu da kuma sauran fuskokin taimakekeniya tsakanin kasashen biyu.

Ziyarar Juna:

  • Tsohon ministan harkokin waje ya kai ziyara kasar Tanzaniyya a cikin Fabrairu shekara ta 2014, don ya mika wasika da rubutun hannu daga tsohon shugaban kasar Misra Adli Mansur zuwa tsohon shugaban Tanzaniyya.
  • Tsohon fira-minista mai girma ya kai ziyara kasar Tanzaniyya a watan Afrilu shekara ta 2014, domin haratar bikin mai lamba 50 na  kasar Tanzaniyya bayan hadakar da ta hade tsakanin “Tanganyika” da “Zanzibar”.
  • Ministan harkokin waje na kasar Tanzaniyya ya kai ziyara kasar Misra a watan Yuni shekara ta 2014, domin halartar bikin nada shugabankasa Abdul Fattah Sisi.
  • Shugaban kasar Misra Abdul Fattah Sisi ya sadu da tsohon sugaban kasar Tanzaniyya a karshen taron kolin kungiyar tarayyar Afrika.
  • Ministan noman na kasar Misra ya kai ziyara kasar Tanzaniyya a watan Nuwamba shekara ta 2015, domin halartar bikin nada shugaban kasar Tanzaniyya.

 

Dangantakar Tattalin arziki:

  • Karfin kasuwanci tsakanin Misra da Tanzaniyya ya kai miliyan talatin da shidda (36m dolla) a 2014 (sayo kaya daga Misra 28m USD, shiga da kaya cikin Misra 8m USD).
  • Irin kayan da Misra take fitarwa zuwa Tanzaniyya sun hada da sukar da sodium carbonate. Kayan da Misra ke shigowa da su daga Tanzaniyya sun hada da jan karfe (copper).

 

Kungiyar Fasaha da Tallafawa:

  • Hukumar hadin- gwiwa don ayyukan raya kasa a Misra ta gabatar kwasa-kwasai da guraben karatu da Karin ilimi a cikin kasar Tanzaniyya a fannoni daban daban, Bugu da kari kuma da guraben karatu wadanda ma'aikata da Kungiyoyi daban daban a kasar Misra suke gabatar da tuntubar juna tare da ma'aikatar harkokin waje da suke kunshi ma'aikatar wutar lantarki da ma'aikatar albarkatun ruwa da noman rani.
  • An bude cibiyar Musulunci ta kasar Misra a Darus Salam shekara ta 1968. Wannan cibiya tana daya daga cikin alamomin taimakekeniya tsakanin Misra da Tanzaniya ta inda sama da dalibai 1400 suke karatu a cibiyar a marhalolin karatu daban daban daga marhalar firamare har ta sakandire.