Dangantaka Tsakanin Misra da Togo
Litinin, 14 Janairu, 2019
Dangantaka Tsakanin Misra da Togo

Tsokaci kan dangantaka tsakanin kasashen biyu:

Dangantaka tsakanin kasashen biyu ta fara ne tun tale-tale, a lokacin da kasar ta Togo ta samu 'yancin kan ta a shekrara 1960, tun a wancan lokacin Misra ta bude ofishin jakadancinta a kasar Togo, koda yake ita kasar ta Togo ba ta bude na ta ofishin ba tun wancan lokacin, sai dai a shekarar 2004, Togo ta umurci jakadanta na kasar Libya da ya zama mai wakiltan ta a kasar Misra, sannan kuma Gwamnatin Misra ta amince da hakan.

A bangaren siyasa kuwa kasashen biyu na dasawa sosai, domin kuwa ra'ayinsu na zama iri daya a sassa da yawa cikin al’amuran da suka shafi yankuna da kuma kasa da kasa, bugu da kari kasar Togo ba ta yi wa kasar Misra zagon kasa a duk wani al’amari da ya shafe ta, haka kuma kasar Togo ta nuna goyon bayanta ga duk wani kuduri ko wani matsayi da Misra ke nema a matakai na yankuna da kuma kasa da kasa.

Musayan ziyarce -ziyarce tsakanin jami'an kasahen biyu :

 • A ranar 10 ga watan Afrilu ne shugaban kasar Togo Faure Gnassingbé ya kai ziyara kasar Misra, inda shugaba Abdulfattah El'sisi ya tarbe shi da kansa, a yayin ganawar shugabannin biyu sun tattauna kan lamuran da suka shafi kasashen biyu ta fuskoki da dama, tare da bincika hanyoyin da za su kara inganta dangantakar kasashen biyu, haka nan sun tattauna kan lamuran da suka shafi Nahiyar Afirka da kuma kasa da kasa wanda kasashen biyu suke da hannu a ciki, musamman inganta harkokin tattalin arziki da zamantakewa, gami da yaki da ta'addanci da kuma kawar da talauci a tsakanin a'umma.
 • A ranar 4 ga watan Maris na shekarar 2016, Injiniya Ibrahim Mahlab mataimakin shugaban kasar Misra mai kula da ayyukan raya kasa da cigaban yankuna ya kai ziyara kasar Togo sakamakon gayyatar da Shugaban kasar Faure ya yi wa Gwamnatin kasar Misra, a lokacin ne Injiniya Ibrahim Mehlab ya mikawa shugaban kasar sako cikin takarda daga shugaba Abdulfattah El'sisi, takardar ta kunshi yanda kasashen biyu za su karfafa dangartakarsu ta fuskar sufuri na kan tudu, zirga zirgan jiragen sama, kiwon lafiya, noma, makamashi, gidaje, da kuma yawon bude ido.
 • A ranar 21 ga watan Fabrairu na shekarar 2016, Fira-ministan kasar Togo Komi Seilom Klaso ya kai ziyara kasar Misra domin halartan taron kasashen Afirka kan tattalin arziki na shekarar 2016 da ya gudana a Sharm El'sheikh na kasar Misra, inda suka tattauna da shugaba Abdulfattah El'sisi kan abubuwan da dama da kasashen biyu suka hadu akai.
 • Tsohon ministan harkokin kasashen waje na Togo kuma mai bai wa shugaba Faure Gnassingbé shawara kan siyasa Koffi Essaw ya kai ziyara Misra inda ya ya da zango a Sharm El'sheikh domin halartan taron shirye -shiryen taron kolin kasashe 'yan ba ruwanmu da aka yi a ranakun 13 - 14 - 2009.
 • Ministan yawon bude ido na kasar Togo ya kawo ziyara kasar Misra a watan Maris na shekarar 2009, inda ya tattauna da takwarar aikinsa na Misra har suka rattaba hannu kan wasu yarjejeniyoyi kan yawon bude ido tsakanin kasashen biyu.
 • Ministan makamashi da ma'adinai na kasar Togo ya kawo ziyara AlKahira domin halartan wani taro na ministocin makamashi na Afirka wanda ya gudana a kasar Misra.
 • Mai bai wa shugaban kasa shawara kan siyasa ya ziyarci Misra a ranar 21 ga watan Fabrairu na shekarar 2005, bayan rasuwar shugaban kasar Eyadema.
 • Mataimakin minsitan Harkokin wajen na Misra mai kula da al'amuran Afirka da kungiyar tarayyar Afirka ya kai ziyara kasar Togo a ranakun 2 zuwa 4 na watan Nuwamban shekarar 2007, a lokacin ya gana da babban sakataren ma'aikatar Harkokin wajen Togo tare da ministan lafiyar kasar.
 • Shugaba Faure Gnassingbé ya kawo ziyara Misra a watan Yuli na shekarar 2007, domin halartar taron koli na kungiyar tarayyar Afirka.
 • Ziyarar mataimakiyar minsitan Harkokin wajen Misra mai kula da kasashen Afirka da kungiyar tarayyar Afirka zuwa kasar Togo tsakanin 21 - 23 na watan Oktoba na shekarar 2010, inda ta samu ganawa da firaministan kasar Togo tare da shugaban kotun tsarin mulki na kasar, haka nan ta gana da mataimakin shugaban majalisar Dokokin kasar, bugu da kari ta tattauna da ministocin tsaro, yawon bude ido, da na kiwon lafiya, sannan ta zanta da jami'an ma'aikatan Harkokin wajen kasar Togo inda suka tattauna kan muhimman abubuwa da suka hada kasashen biyu wuri daya, kamar yanda suka tattauna kan matsayin kasashen biyu kan lamuran da suke faruwa a yankin yammacin Afirka.

 

Dangantakar kasashen biyu kan tattalin arziki :

 • A ranar 19 ga watan Fabrairu na shekarar 2017, Ministan zirga zirgan jiragen sama na Misra Sharif Fathy tare da minsitan sufurin Togo Juno Fam sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya kan bayar da horo da ingancin zirga zirgan jiragen sama tare da samar da tsaro kan haka.
 • A ranar 10 ga watan Afrilu na shekarar 2016, shugaba Abdulfattah El'sisi na Misra tare da shugaba Faure Gnassingbé na Togo sun rattaba hannun kan wasu yarjejeniyoyi guda hudu na fahimtar juna a tsakaninsu, yarjejeniyoyin sun shafi gine gine da raya birane, ministan harkokin wajen Misra Sameh Shukry ne ya sanya hannu a madadin kasar Misra, yayin da ministan gidaje da raya birane na kasar Togo Kabo Siseno ya sanya hannu a madadin kasar Togo, yarejejeniyoyin sun hada da :

1 - Taimakekeniya kan lamuran da suka shafi wasanni tsakanin ma'aikatar matasa da wasanni na Misra da kuma ma'aikatar yada labarai wayewa matasa da wasanni na kasar Togo, ministan matasa da wasanni na kasar Misra Khalid AbdulAzeez ne ya sanya hannu a madadin kasar Misra, yayin da ministan yada labarai wayewa matasa da wasanni na kasar Togo ya sanya hannu a madadin kasar Togo.

2 - Taimakekeniya a fannin wayewa, inda ma'aikatar wayewa ta kasar Misra tare da ma'aikatar yada labarai wayewa matasa da wasanni na kasar Togo, ministan wayewa na kasar Misra Hilmy Nimnim shi ne ya rattaba hannu a madadin kasar Misra, yayin da ministan yada labarai da wayewar matasa da wasanni na kasar Togo ya rattaba hannu a madadin kasar Togo.

3 - Taimakekeniya kan yada labarai, tsakanin hukumar bayar da bayanai ta kasar Misra tare da hukumar kula da wayewa ta kasar Togo su ka rattaba hannu a kan haka, shugaban hukumar bayar da bayanai na Misra jakada Salah Abdussadik shi ne wanda ya sanya hannu a madadin kasar Misra, yayin da ministan yada labarai wayewar matasa da wasanni na kasar Togo ya sanya hannu a madadin kasar Togo.

4 - Taimakekeniya a sashen aikin radiyo da talabijin, tsakanin hukumar yada labaran radiyo da talabijin na kasar Misra da ma'aikatar yada labarai wayewa matasa da wasanni suka rattaba hannu kan hakan, Esam Al'Ameer ne ya sanya hannu a madadin kasar Misra, yayin da ministan yada labarai da wayewar matasa da wasannin kasar Togo ya sanya hannu a madadin kasarsa.

5 - Kamfanin shigar da kayayyaki da fitarwa mai suna "Nasr" na zama kamar tsaka-tsaki wurin shigar da amfanin gona na musamman zuwa kasar Togo, kamar cofe da coco, tare da shigar da su zuwa kasashen Turai.

 

Kwamitocin da kasashen biyu suka kafa domin yin aiki tare:

 • An kafa kwamitin aiki tare tsakanin kasashen biyu ne a watan Fabrairu na shekarar 1988.
 • An yi taron farko karkashin wannan kwamiti ne a watan Fabrairu na shekarar 1988 a birnin Alkahira.
 • An yi taro kashi na biyu karkashin wannan kwamiti a watan Janairun shekarar 1991 a Lome.

 

Tsare -tsaren cinikayya tsakanin kasashen biyu :

 • An cinma yarjejeniyar samar da kwamitin da zai yi aiki tsakanin kasashen biyu.
 • Amincewa da yin aiki tare a sashen wayewa wanda aka rattabawa hannu a ranar 17 ga watan Maris na shekarar 1964, sannan yarjejeniyar ta fara aiki ne a shekarun 1991- 1992 - 1993.
 • Yarjejeniya kan kasuwanci wanda aka sanya wa hannu a ranar 17 ga watan maris na shekarar 1981.
 • Yarjejeniya kan tattalin arziki da kimiyya wanda aka sanya hannu ranar 27 ga watan Janairu na shekarar 1981.
 • Yarjejeniyar yin aiki tare a bangaren aikin soja wanda aka sanyawa hannu a ranar 18 ga watan Afrilu na shekarar 1981.
 • Yarjejeniya kan ayyukan fasaha wanda aka cim ma wa tare da Asusun bayar da taimakon fasaha tare da Afirka, ya samu sanya hannu a ranar 6 ga watan Fabrairun shekarar 1988.
 • Yarejejeniyar tafiye tafiye kan ruwan, ya samu sanya hannu a ranar 6 ga watan Fabrairun shekarar 1988.
 • Kulla yarjejeniyar taimakekeniya kan yawon bude ido, an sanyawa yarjejeniyar hannu a ranar 26 ga watan Maris na shekarar 2009.

 

Dangantakar wayewa da fasaha tsakanin kasashen biyu :

 • A kasar Togo akwai wata tawaga ta Al-Azhar da ta kunshi malamai da suke aikin yada Addinin Musulunci a kasar tare da koyar da Musulmai shari'ar Musulunci tare da koya musu Harshen Larabci da koya musu karatun Alkur'ani mai girma a makarantun Islamiyoyi da suke sassa da dama na kasar Togo, haka nan Al-Azhar na bai wa 'yan kasar tallafin karatu da kuma gurbin yin karatu a tsangayoyin jami'ar da dama.
 • Kasar Togo na samun gayyata koda yaushe domin halartan samun horo kan abubuwa da yawa wanda Hukumar bunkasa yankuna ta kasar Misra take gabatarwa da suka hada da samun horo na aikin 'yan sanda, noma, shari'a, kiwon lafiya, aikin unguwar zoma, aikin yada labarai, da kuma ayyukan diflomasiyya, haka nan wannan Hukumar ta kasar Misra na taimaka wa kasar Togo da kayayyakin bukata na aikin asibiti da magunguna tare da kayayyaki masu matukar muhimmanci.