DANGANTAKAR KASAR MISRA DA ERITREA
Laraba, Maris 06, 2019
DANGANTAKAR KASAR MISRA DA ERITREA

DANGANTAKAR KASAR MISRA DA ERITREA

Gabatarwa :

Kasar Misra na da kyakkywar dangata da kasar Eritrea na tsawon lokaci, domin kuwa Misra ta taka - rawar - gani sosai wurin nuna goyon bayanta ga juyin juya halin kasar har zuwa lokacin samun 'yancin kan kasar a shekarar 1993. Haka nan Misra ta cigaba da nuna goyon bayanta ga kasar ta Eritrea yayin gwagwarmayar neman 'yanci har zuwa bayan haka, har wala yau ta kasance cikin kasashen da suka nuna farin cikinsu da samun 'yancin kan kasar tare da fatan samun kyakkyawar dangantaka na cigaba da taimakekeniya a sassa da dama tsakanin kasashen biyu.

Dangartakar siyasa tsakanin kasashen biyu :

Kasar Misra na mai da hankali sosai akan al’amuran da suka shafi kasar Eritrea tun daga shekarar 1940 na karnin da ya gabata. Bayan samun 'yancin kan kasar Eritrea kasar Misra ta yi maraba da samun kyakkyawan dangantaka tsakaninta da Eritrea, domin hakan ya zama tsaftatacciyar hanyar kulla dangantaka tsakanin Alkahira da Asmara.

Dangantakar da take tsakanin kasashen biyu ta taka rawa sosai wurin daidaita al’amura yayin rikicin kan iyakar kasar Eritrea da Ethiopia na tsawon shekaru biyu, daga (1998 - 2000), domin kuwa Misra ta yi iya bakin kokarinta na sulhunta kasashen biyu.

Tun bayan samun 'yancin kan kasar Eritrea shugaban kasar Asyas Aforki ya kawo ziyara zuwa kasar Misra har sau 16, a ziyarar karshe ne shugaban ya gana da shugaba Abdul fatah Elsisi a watan Nuwamba ta shekarar 2016, inda shugabannin biyu su ka tattauna akan abubuwan da za su kara karfafa dangantakar da take tsakanin kasashen biyu a sashen siyasa da tattalin arziki, bugu da kari, sun tattauna akan yanda za a warware matsalolin yankin kahon Afirka tare da yaki da ta'addanci da wuce gona da iri da sunan Addini.

Ziyarce ziyarcen juna :

Kasashen Misra da Eritrea sun ziyarci juna da daman gaske domin karfafa dangantar da take tsakaninsu, tare da kokarin fuskantar al'amuran da kasashen biyu suke da abin cewa a ciki musamman ma cikin abubuwa masu zuwa :

  • A ranar 13 ga watan Satumba na shekarar 2018 ministan harkokin kasashen waje na Misra Sameh Shukry ya kai ziyara Asmara inda ya mika sakon baka daga shugaba Abdulfattah Elsisi zuwa shugaba Asyas Aforki, sakon ya kunshi kyautata dangantaka ne tsakanin kasashen biyu, tare da tabbatar da an cimma yarjejeniyoyin da kasashen biyu suka sanya hannu akai a baya na sassa da dama, hakan nan sakon ya kunshi al'amuran da suka shafi matsalolin kasa da kasa wanda kasashen biyu suke tarayya ciki.
  • A ranar 9 ga watan Janairu na shekarar 2018 shugaban kasar Eritrea Asyas Aforki ya kawo ziyara birnin Alkahira inda - lokacin ziyarar - ya gana da shugaba Abdulfattah Elsisi inda suka tattauna akan dangantakar da take tsakanin kasashen biyu, tare da bitar cigaban da aka samu a baya, hakan nan sun tattauna akan matsalolin da suke tattare da kasashen da suke daura da kogin Nilu da kuma kasashen da suke yankin kahon Afirka gami da al’amuran da suka shafi kasa da kasa wadanda kasashen biyu suke tarayya a ciki.
  • A ranar 6 ga watan Mayu na shekarar 2017 ministan harkokin kasashen waje na Eritrea Usman Saleh tare da Yamani Jebryab sun kawo ziyara kasar Misra inda ministan harkokin waje Sameh Shukry ya tarbe su, bayan haka sun tattauna akan yanda za a karfafa dangantakar da take tsakanin kasashen biyu a sassa da daman gaske wanda suka hada kasashen biyu wuri daya, kasashen biyu na dasawa sosai a sashen diplomasiyya na tsawon tarihi.
  • A ranar 19 ga watan Maris na shekarar 2017 wata babbar tawagar kasar Eritrea ta kawo ziyara kasar Misra, tawagar ta kunshi ministan harkokin waje Usman Saleh da mai bai wa shugaban kasar shawara a bangaren siyasa da tattalin arziki Yamani Jebryab da Hajos Jabrhwet, wannan tawaga ta tattauna da bangaren kasar Misra akan dangantakar da take tsakanin kasashen biyu, tare da al'amuran da suka shafi kasa da kasa wadanda kasahen biyu suke tarayya ciki, haka nan sun tattauna kan matsalolin yankin Bahr Maliya da kuma cigaban da ake samu na zaman lafiya a kasashen Yamen da Somalia da kuma Kudancin Sudan, haka kuma sassan biyu sun shawarta da juna kan yanda za su tunkari al'amuran kasa da kasa da suke da hannu ciki, haka nan sun tattauna kan takunkumin da kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya sanyawa kasar ta Eritrea.
  • A ranar 29 ga watan Nuwamba na shekarar 2016 shugaba Abdulfattah Elsisi ya karbi bakoncin shugaba Asyas Aforki na Eritrea yayin ziyararsa zuwa birnin Alkahira inda shugabannin biyu suka tattauna akan al'amuran da suka hada kasahen biyu akai, tare da tattauna matsalolin da kasashen Afirka suke fuskanta musamman yankin kahon Afirka.
  • A ranar 7 ga watan Mayu na shekarar 2015 ministan harkokin wajen Misra Sameh Shukry ya kai ziyara Eritrea inda ya gana da ministan harkokin wajen kasar Usman Saleh da mai bai wa shugaban kasar shawara kan harkokin siyasa Yamani Jebryab, sassan biyu sun tattauna akan abubuwan da suka hada kasashen biyu akai ta kowace fuska, tare yin nazari akan yadda za a sake inganta dangantakar da take tsakanin kasashen biyu, sannan kuma sun tabo al’amuran da suka shafi kasa da kasa wadanda suke da ta cewa a cikinsu, musamman rikicin kasar Yamen da samar da ingantaccen tsaro a yankin Bahr Maliya, sannan kuma sun cimma yarjejeniyar yin aiki tare wurin yaki da ta'addanci da samar da zaman lafiya a yankin kahon Afirka da yankin Gabas ta Tsakiya.
  • A ranar 9 ga watan Satumba na shkerar 2014, shugaba Asyas Aforki ya jagoranci wata tawagar kasar Eritrea zuwa kasar Misra wacce ta hada da ministan harkokin wajen kasar Usman Saleh da mai bai wa shugaban kasar shawara akan harkokin siyasa Yamani Jibryab, tare da jakadan kasar Eritrea a Misra Fasil Jebselasy da sakataren yada labarun shugaban kasa Al'ameen Hassan, inda sassa biyu suka tattauna akan dangantakar da take tsakaninsu, da kuma matsalolin kasashen Afirka musamman wurin yaki da ta'addanci da kuma tsattsauran ra'ayin Addini da kawo karshen fashin teku a gabar kasashen da suke yankin, bakin shugabannin biyu ya zo daya wurin kara kusantar juna da tuntubar sauran kasashen Afirka domin samun nasara akan wadannan abubuwa da za su tabbatar da zaman lafiya gami da kwanciyar hankali a nahiyar Afirka.

Dangantakar cinikayya tsakanin kasashen biyu :

Karfin cinikayya tsakanin kasashen biyu ta kai kololuwarta; domin kuwa Misra na shigar da kayanta zuwa Eritrea da suka kai kimanin Dalar Amurika Miliyan 47.79, na kayayyakin da suka hada da: danyan garin fulawa, ko kuma busasshe da kuma sinadarin hada fyanti, da kuma curarren jubna na karin kumallo, sai kuma siminti, haka nan kuma Misra na shigo da kayayyaki daga Eritrea na kimanin Dalar Amurika miliyan 5.6, kayayyakin sun hada da: tsimi da danyen bunni, wanda hakan ya ingiza yawan ribar da Misra take samu a wannan cinikayya da kimanin Dalar Amurika Miliyan 42.

Taimakekeniya a harkar kiwon lafiya :

  • A irin kyakkyawar dangantakar da take tsakanin kasar Misra da Eritrea, Hukumar kula da taimakekeniya akan bunkasa kasashe na kasar Misra da take karkashin ma'aikatar harkokin kasashen waje ta tura wata tawagar likitocin ido zuwa kasar Eritrea a tsakanin 28- 4 - 2017 zuwa 7 - 5- 2017, tare da gudunmawar ma'aikatar kiwon lafiyar kasar Misra inda aka tura likitocin ido guda huda (4) tare da injiniyan saffara na'aurar aikin ido zuwa kasar domin duba lafiyar idanun 'yan kasar kyauta. Ministar kula da kiwon lafiyar kasar Eritrea Amina Nour Husain ita ce ta tarbi wannan tawaga ta kasar Misra a farfajiyar ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar da take Asmara, inda ta nuna matukar jin dadinta akan yanda Misra take bayar da gudunmawa ga kasar Eritrea musamman a sashen kiwon lafiya, sannan ta yi maraba da duk wani taimakekeniya da zai cigaba da wanzuwa tsakanin kasashen biyu, tare da fatan samun bakoncin wata tawagar nan gaba, musamman a sashen aikin ido. Wannan tagawar ta likitocin ido ta samu nasarar duba lafiyar daruruwan masu fama da ciwon ido a kasar, game da yi wa mutane da yawan gaske aiki a idonsu yayin kasancewar tawagar a kasar ya Eritrea a babban asibitin ido na kasa da yake
  • Hakan nan ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Misra tare da gudunmawar Hukumar kula da taimakekeniya kan bunkasa kasashe na kasar Misra da take karkashin ma'aikatar harkokin kasashen waje ta tura wata tawagar kwararrun likitoci zuwa birnin Asmara da ke kasar Eritrea a tsakanin 27 ga watan Mayu zuwa 10 ga watan Yuni na shekarar 2016, domin bayar da agaji ga al'ummar kasar Eritrea a bangaren kiwon lafiya, tawagar da kunshi likitoci Takwas (8) da suka kware a fannonin kiwon lafiya da dama, tare da injiniya mai kula da na'urorin kiwon lafiya, wannan tawagar ta kai ziyara zuwa asibitoci uku (3) da suke Asmara, inda suka yi wa mutane (105) aiki, sannan suka duba marasa lafiya (1200), har wala yau sun yi aikin ido ga wasu cikin marasa lafiyar da kuma gyara na'urorin da ma'aikatar kiwon lafiyar kasar suke amfani da su.