Dangantakar Kasar Misra Da Namibia
Asabar, Fabrairu 09, 2019
Dangantakar Kasar Misra Da Namibia

Kasar Misra na daya daga cikin kasashe na farko da suka fara kulla dangantaka ta jakadanci da kasar Namibia tun bayan samun 'yancin kanta a shekarar 1990, daga nan kasar Namibia ta turo jakadanta na farko zuwa birnin Alkahira da yankin Gabas ta Tsakiya a watan Afrilu na shekarar 2008, wannan na zuwa ne bayan samar da jakadanci a Alkahira da Gabas ta Tsakiya tun a shekarar 2007, haka nan Misra ta taka-rawa sosai wurin taimaka wa masu fafutukar neman 'yancin Namibia da aka fi sani da suna (Swabo) yayin neman 'yancin kansu a wurin Hukumar wariyar launin fatan kasar Afirka ta Kudu. Har wala yau, Misra ta taka-rawar gani wurin taimaka wa Namibia a duk wani bigire na kasa da kasa, musamman ma a zauren majalisar Dinkin Duniya, Haka nan Misra ta mika gudunmawa na kayayyaki da yawa ga kasar ta Namibia, kamar yanda - har wala yau - ta taimaka wurin bayar da horo na musamman ga masu fafutukar yaki da wariyar launin fata 'yan Namibia lokacin shugabancin Jamal Abdunnaseer, ko ba komai dai a birnin Alkahira aka fara bude ofishin fafutukar neman 'yancin kasar Namibia (Swapo).

Dangantakar siyasar kasashen biyu na da matukar karfi sosai, domin kuwa an gayyaci Misra halartan taron murnan samun 'yancin kan kasar Namibia a shekarar 1990, a matsayinta na shugabar Hadin kan kasashen Afirka a wancan lokacin, kuma Misra ta ci gaba da bai wa kasar Namibia gudunmawa a siyasance da tattalin arziki bayan samun 'yancin kanta.

Har wala yau, shugaban kasar Namibia "Hifikepunye Pohamba" ya aiko wa Shugaba Abdulfattah Elsisi sakon taya murna a ranar 19 ga watan Yuni na shekarar 2014 bayan rantsar da shi a matsayin shugaban kasa.

 

AYYUKAN BAYAR DA HORO TSAKANIN KASASHEN BIYU

An samu nasarar rattaba hannu a wata yarjejeniya tsakanin kasashen biyu a bangaren aikin Diplomasiyya, wanda ministocin kasashen waje na kasashen biyu suka cimma wa, sannan kuma aka samu wani bigiren a sashen kara wa juna sani, tare da bai wa tsaka-tsakin jami'an Gwamnati horo na musamman akan ayyukan kasashen waje,
da manyan jami'an a sashen ayyukan kasa da kasa, a bigire na karshe kuma kasar Misra ta bayar da horo ga  jami'an kasar Namibia guda 170, a bangarori da yawa, da wannan ne kasar Namibia ta zamo cibiyar bayar da horo na kara wa juna sani a Nahiyar Afirka.

Cibiyar kasar Misra mai bayar da tallafin ayyukan gona da kiwo da "su" wato (kamin kifi), ta bayar da tallafi ga kasar ta Namibia.

Da yawa 'yan jaridar kasar Namibia na samun horo kan aikin jarida da kungiyar 'yan jaridar Afirka take shiryawa duk shekera a kasar Misra tun bayan samun 'yancin kasar a shekarar 1990.

 

TALLAFI NA KARATU :

Kasar Misra ta amince da bayar da tallafin karatu 5 ga 'yan kasar Namibia don yin karatu a jami'o’in Misra a bangarori da dama kamar : injiniya, ilmin sanin kasa, haka nan mutum 2 na samun tallafin karatu a Jami'ar Al Azhar a duk shekara.

 

ZIYARCE-ZIYARCE TSAKANIN KASASHEN BIYU

Shugaban kasar Namibia Hage Geingob ya ziyarci Misra inda ya halarci taron kungiyoyin kasashen Afirka uku da ya gudana a garin Sharm El'Sheikh na Misra a watan Yuni na shekarar 2015.

Wata tawagar kasar Namibia karkashin ministan Harkokin wajen kasar Atony Nyuma ta ziyarci Misra a ranar 31 ga watan Oktoba zuwa 2 ga watan Nuwambar shekarar 2010, a lokacin sun tattauna da ministocin kasar Misra na Harkokin kasashen waje, kasuwanci da masana'antu, noma da kiwo, yayin halartar taron kasashe 'yan ba ruwanmu da aka yi a watan Yuni na shekarar 2009 a Sharm El'sheikh.

 Wata tawaga karkashin ministan Harkokin wajen kasar Namibia ta kawo ziyara kasar Misra domin halartan taron kasashen Afirka da China a shekarar 2009 a garin Sherm El'sheikh.

Wata tawagar kasar Namibia karkashin ministan kasuwanci da masana'atu Dakta Hage Geingob ta kawo ziyara kasar Misra domin halartan taron ministocin kasuwanci na Afirka da ya gudana daga 27 zuwa 29 na watan Oktoba na shekarar 2009 a birnin Alkahira.

Wata tawagar kasar Namibia karkashin ministan ilimi ta kawo ziyara kasar Misra a watan Fabrairun shekarar 2008, domin tattaunawa da jami'an Misra kan harkokin ilimi tare da taimakekeniya a sashen karantarwa da kuma tsarin karatun jami'a.

Wata tawagar kasar Namibia ta kawo ziyara karkashin jagorancin minsitan kiwon lafiya Dakta Richad Kamoi a watan Oktoba ta shekarar 2008, domin taimakekeniya a sashen kiwon lafiya tsakanin kasashen biyu.

Shugaban Majalisar Dokokin kasar Namibia Dakta Thiu Bn Jorirab - a matsayinsa na shugaban kungiyar 'yan majalisun kasashen Duniya - ya kawo ziyara kasar Misra a watan Disamba ta shekerar 2008 domin yin bincike kan laifukan yaki a yankin zirin Gazza.

Mataimakin ministan Harkokin kasashen wajen Misra mai kula da kasashen Afirka da kungiyar tarayyar Afirka, tare da mataimakin mai kula da yankin Gabashi da Kudancin Afirka sun kai ziyara birnin "Walfesh Bai" na kasar Namibia inda suka rattaba hannu a kan abubuwa da dama musamman harkokin ilimi da ma'adinai, haka kuma sun tattauna kan kasuwanci da siyasa.

Wata tawagar kasar Misra ta kai ziyara kasar Namibia karkashin sakataren Asusun bayar da tallafi kan fasaha tare da Nahiyar Afirka a ranakun 2 zuwa 3 na watan Maris na shekarar 2009, inda suka gana da ministocin Noma da kiwon lafiya.

Wata tawaga ta kai ziyara domin halarta karo na Goma sha Tara a "Wondkok" na shugabannin yaki da shan miyagun kwayoyi na kasashen Afirka (Holena) a tsakanin ranakun 12 zuwa 16 na watan 10 ta shekarar 2009.

DANGANTAKAR TATTALIN ARZIKI

Ana shigar da kayyakin kasar Misra zuwa Namibia daga kasar Afrirka ta Kudu saboda saukin zirga-zirga, haka nan an kulla yarjejeniyar shigar da kayayyakin kasar Misra kai tsaye zuwa Namibia kamar su "magunguna, wayoyin lantarki da kuma kayan makamashin samar da wutar lantarki.

Duk da ana samun tsaiko da wahala na musanyen kasuwanci tsakanin kasashen biyu sosai, sakamakon rashin yawan mutane a kasar Namibia, domin dududu mutanen kasar ba su wuce miliyan biyu ba, wadanda ke warwatse a farfajiyar kasa mai fadin kilomita Dubu daya da Dari Takwas da Ashirin da Hudu, (1,824) murabba'i.

DANGANTAKAR CINIKAYYA TSAKANIN MISRA DA NAMIBIA

Muhimman kayayyakin da ake shigarwa daga Misra zuwa Namibia ko ake shigarwa Misra daga Namibia :

MUHIMMAN KAYAYYAKIN DA MISRA KE KAI WA :

Kayayyakin karau, mai na motoci da gris, bututaye na roba da karfe, kayayyakin ado na katako tare da magunguna.

ZUBA HANNAYEN JARIN MISRA A NAMIBIA :

Akwai hannayen jarin kasar Misra da yawa a Namibia da suka hada da ayyukan "sadarwa, domin kuwa kamfanin (Telecel) da ke zama wani sashe ne na kamfanin (Orascom) da wani dan kasuwa mai suna Najeeb Swares ke mallakan kamfanin, shi ne ya  siya kamfanin (Cell One) domin aikin sadarwar wayar hannu da kimar kudin ya kai kimanin Dalar Amurka Miliyan 88, daga baya sai aka sauya alamar kasuwancin kamfanin zuwa (Leo).

Akwai ayyukan zuba hannayen jari na 'yan kasar Misra da ke aiki a Arewacin kasar a sashen noman rani wanda kudin da aka sanya cikin wannan harka ya kai Dalan Amurka miliyan 60, sannan kuma akwai 'yan kasuwan Misra da yawa da suke aikin shigarwa da fitarwa na kayyaki na aikin injiniya tsakanin kasashen biyu.