Dangantakar Tsakanin Misra da Jamhuriyyar Kongo Dimokradiyya
Laraba, 2 Janairu, 2019
Dangantakar Tsakanin Misra da Jamhuriyyar Kongo Dimokradiyya

Takaitaccen Tarihi:

Dangantakar da take tsakanin Misra da Jamhuriyyar Kongo Dimokradiya ta fara tun daga shekara ta 1960, lokacin da Misra ta tallafa wa Kongo wajen fafutukar neman 'yanci kai. Misra ta karbi iyalan Patrice Lumumba, fira-minista na farko lokacin da ake kasha shi bayan ya yi zaman gidan yari. A koda yaushe, Misra tana taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da cigaban DRC (Democratic Republic of the Kongo) wanda har yanzu hakan yake, a inda Misra take sa baki a majalisar Dinkin Duniya da kuma majilisar ta kungiyar tarayyar Afrika.

A yanzu haka dangantakar da take tsakanin Misra da DRC na bisa turbar nasara. Bugu da kari Misra na fifita samar da kyakkyawan ilmi da karfafawa da gina mutanen.

Ziyarar Juna:

Halartar mai girma shugaban kasa Joseph Kabila wurin kaddamar da bukin samar da sabuwar hanyar ruwa a watan Augusta shekara ta dubu biyu da goma sha biyar (2015) a lokacin da kasashen suka sa hannu a takardar amincewa wajen taimakon juna a fannonin makamashi, muhalli da lafiya tsakaninsu.

Ziyarar mai girma fira-minister DRC Augustin Matata Poryo zuwa Misra a cikin Fabrairu shekara ta dubu biyu da goma sha shidda (2016) fira- ministocin sun rubuta takardar hadin gwiwa akan abin da ya shafi sa hannun Misra a mataki na 3 da na 4 na ginin “Inga Dan” a kogin Kongo, baya ga sa hannu a takardun yarjejeniya ta fahimta tsakanin hukumar Hanyar Ruwan Suez da matsayar hukumar cigaban Inga.

Shekara biyu da suka wuce, an sami ziyarce- ziyarce da yawa daga manyan ma'aikata gwamnatin Misra zuwa Ruwanda  akan abubuwan da suka shafi kasashen biyu ko kuma fiye da haka, hade da ziyarar tsohon ministan harkokin kasashen tsallake na Kinshasa da goma a cikin watan Fabrairu, 2014 da kuma ziyarar ministan noman rani da albarkatan ruwa a watan Mayu 2015.

Manyan Jami'an gwamnati na Kongo sun kai ziyarce –ziyarce  da yawa a kasar Misra dangane haka, tare da ziyarar minista muhalli da adana ma'adinai a watan Yuni 2015, mataimakin minista harkokin kasashen ketare a Augusta 2015.

Tattalin Arziki

Karfin kasuwanci tsakanin Misra da DRC ya kai miliyan sittin da biyar (65m dolla) a 2014 (sayo kaya daga Misra 35m USD, shiga da kaya cikin Misra 30m USD)

Irin kayan da Misra take fitarwa zuwa DRC sun hada da fruit juice da vegetable saps da extracts. Kayan da Misra ke shigowa da su daga DRC sun hada da copper da zinc.

Kungiyar Fasaha da Tallafawa

Kungiyar hadin kan Misra don cigaba ta taka muhimmiyar rawa wajen gina mutane a DRC ta hanyar aiwatar da kwasa-kwasan horaswa tare da hadin guiwa da manyan jama'ai da suke da masaniya akan kwasa-kwasan da suke kunshi fannin lafiya, wutar lantarki, noman rani, noma da jakadanci.

Wannan kungiyar dai, ta ba da tallafi ga fannoni da yawa a DRC wadanda suka hada fiye da shekara uku wajen farfado da gyaran sassa a babban asibiti gwamnati ta Kinshasa, tare da ba su kayyayakin aiki na asibiti. Haka kuma kungiyar masana harkar lafiya don taimakewa da kuma samar da wurin horar da mutane a Kinshasa.

Kwamitin kirkira da cigaba kasashen gefen kogin Nil yana aiwatar da ayyuka da yawa a DRC wadanda suka hada da samar da gona ta zamani, tashar hasken wutar lantarki da babbar asibiti a Kinshasa.