Dangantakar tsakanin Misra da Kenya
Laraba, 2 Janairu, 2019
Dangantakar tsakanin Misra da Kenya

Takaitaccen Tarihi:

Dangantakar kasar Misra da kasar Kenya dangantaka ce ta musamman da take da ta-gomashi mai yawa; saboda soyayya da taimakekeniya da suke a tsakaninsu tun lokacin da aka kafa wannan dangantakar, ta inda kasar Misra ta jajirce wajen taimaka wa mutanen kasar Kenya a lokacin da kasar ta sami kanta cikin matsala. Wannan dangantaka tsakanin kasashen guda biyu ta fara tun karfin kasar Kenya ta sami 'yancin kanta, inda kasar Misra a lokacin shugabancin Jamal Abdul Nasir ta taimaka wa harkar “Maw Maw” da ke kasar Kenya ta fagen siyasa da kafafen yada labarai, wanda wannan harka ta “maw maw” ta karkatar da akalarta don yaki da ‘yan mulkin mallakar Ingila da suke kasar Kenya. A wannan lokaci kasar Misra ta kebence gidan Rediyo da harshen Swahili wanda aka sa masa suna " Muryar Afrika" wannan gidan rediyo shi ne na farko da aka kafa da harshen Swahili a nahiya ta Afrika, domin tamaka wa mutanen kasar Kenya a yakin da suke yi da ‘yan mulikin mallaka.

Kasar Misra ta sanya batun “maw maw” da batun sauke gammon babban batu da ya shafi duk Afrika, ta inda birnin Alkahira ya kasance birni na farko da ya bude kofofinsa ga shugabanni da jagorin kasar Kenya ta hanyar ba su duk wani taimako da ya kamata don harkarsu ta sami nishdi da walwala a cikin kasar ta Kenya daga wadannan jagorori na kasar Kenya. Akwai Ajenga da “Odenja” da “Tom mboya” da “James Jishoro” da “Joseph morobi” da wadasunsu kamar su membobin kungiyar hadin-kan kasar Kenya ta Afrika "kanu" da kungiyar hadin-kan dimokradiyya ta kasar Kenya (KADU) wadannan kungiyoyi sun bude ofisoshi a birnin Alkahira a wannan lokaci.

A shekaru goma da suke wuce kasar Misra ta cigaba da siyasarta ta taimaka wa kasar Kenya ta inda ta ba ta taimako na gaggawa a lokacin da take cikin matsala, don yaki da matsaloli kamar su fari da ambaliyar ruwa, hakan ya faru ne ta hanyar ba ta taimakon abinci da na magani ga mutanen kasar Kenya.

Ziyarce ziyarce da ke tsakanin kasashen guda biyu:

Ministan harkokin waje a lokacin da ya jagoranci wasu manya-manyan mutane ya kai ziyara zuwa Nairobi a watan Janairu shekara ta 2015. A wannan ziyarar ya shugabanci ayyukan Daura ta shida ta kwamitin kasar Misra da kasar Kenya suka yi tarayya a ciki. Haka kuma, ministan harkokin na waje ya hadu da shugaban kasar Kenya da mataimakinsa da ministar harkokin waje ta kasar Kenya, da kuma shugaban majalisar Kenya ta inda ministan ya mika wasika da rubutun hannu daga shugaban kasar Misra zuwa shugaban Kenya.

Ministan harkokin waje da ministan kasuwanci sun kai ziyara zuwa kasar Misra a watan Janairu shekara ta 2015 domin halartar tararrukan kungiyar kasuwanci ta duniya.

Ministan noman na kasar Kenya ya kai ziyara birnin Alkahira a watan Maris shekara ta 2015, a wannan ziyarar ya hadu da masu girma ministocin kasuwanci da kere kere na waje da kasuwanci na gida albarkatun ruwa da noman rani, kamar yadda aka rattaba hannu a karshen ziyarar akan takarda wadda aka kebance ta domin samar da gona ta kowa da kowa a kasar Kenya.

Ziyarar wasu mutane daga majalisar Kenya zuwa kasar Misra a watan Nuwamba shekara ta 2015, wadanda shugaban kasa Abdul Fattah Sisi ya karbi bakwancinsu.

Wata jama'a daga kwalejin sojoji ta kasar Kenya wadda ta kunshi dalibai daga kasashen Afrika daban daban ta kai ziyara zuwa birnin Alkahira a watan Maris shekara ta 2016 a karkashin taron taimakekeniya tare da makarantar  Nasir ta sojoji a wannan lokaci Jakada Hamdee Sanad Liwaz karamin ministan harkokin waje na Afrika shi ne wanda ya tari wadannan tawaga a ziyararsu zuwa birnin Alkahira.

Alakar Tattalin Arziki

Cinikayya tsakanin kasar Misra da kasar Kenya ta kai Dala miliyan 569 a shekara ta 2014 a dunkule kayayyakin da kasar Misra take sana'antawa sun kai Dala miliyan 244, Kenya kuma da kasar take karba daga Kenya sun kai Dala milyan 325.

Kayayyakin da kasar Misra take kai wa zuwa kasar Kenya sun hada da Sikari da takardar lafiya da kayan wanki da allona. Kayayyakin kuma da suke zuwarwa kasar Misra daga kasar Kenya sun hada da shayi da taba.

Taimakakeniyar Karatu Tsakanin Kasashen Guda biyu

Kungiyoyi daban daban a kasar Kenya sun halarci kwasa-kwasai wadanda kungiyar taimakekeniya ta kasar Misra ta gabatar domin samun cigaba a fagen kasuwanci da fasahar kere-kere da noma da hanyoyin zirga-zirga kamar yadda makarantar Misra ta karatun siyasa da cibiyar Alkahira ta kawo zaman lafiya suka shirya a kwasa-kwasai domin 'yan siyasar Afrika daga cikinsu akwai mutanen Kasar Kenya a fagen siyasa da fagen sadarwa da fagen kwantar da tarzoma.

Injiniyoyi guda 25 sun yi karatu a fagen Injinan gona domin karami manomi a karkashin hanzari kasar Misra don cigaba kasashen da suke daura da kogin Nilu  a watan Yuni shekara ta 2014.

Kamar yadda aka sa hannu a takardar fahimtar juna tsakanin kasar Misra da kasar Kenya.

Wani bangare na Kenya ya halarci shirin kwas din da ake duk shekara wanda ma'aikatar wutar lantarki ta kasar Misra a kasashen da suke daura da kogin Nilu ta kaddamar da shi da ma wasu kwasa kwasai da ma'aikatar albarkatun ruwa da noman rani ta gabatar.